1Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
2gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
3Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
4Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
5Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
6Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
7Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
8Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
9Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
10A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba.
11Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.
12Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;
13amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.
14Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.
15Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
16Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;
17gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
18Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.
19A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.
20Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.
21Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;
22waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.
23In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;
24ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
25Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
26Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.
27Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
28Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.
29Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.
30Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
31Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.