📖 Zabura 36
-
1
Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.
-
2
Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
-
3
Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.
-
4
Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.
-
5
Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.
-
6
Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.
-
7
Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.
-
8
Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.
-
9
Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.
-
10
Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.
-
11
Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni.
-
12
Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!