📖 Zabura 34
-
1
Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
-
2
Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
-
3
Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.
-
4
Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.
-
5
Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
-
6
Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.
-
7
Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.
-
8
Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
-
9
Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
-
10
Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
-
11
Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.
-
12
Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
-
13
ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
-
14
Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
-
15
Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
-
16
fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.
-
17
Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.
-
18
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
-
19
Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
-
20
yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.
-
21
Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai.
-
22
Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.