📖 Zabura 33
-
1
Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
-
2
Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
-
3
Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
-
4
Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi.
-
5
Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
-
6
Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
-
7
Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
-
8
Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
-
9
Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
-
10
Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane.
-
11
Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
-
12
Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa.
-
13
Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam;
-
14
daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya,
-
15
shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi.
-
16
Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
-
17
Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
-
18
Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
-
19
don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.
-
20
Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
-
21
A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
-
22
Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka.