📖 Zabura 30
-
1
Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
-
2
Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.
-
3
Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
-
4
Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.
-
5
Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.
-
6
Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”
-
7
Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.
-
8
A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.
-
9
“Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?
-
10
Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”
-
11
Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
-
12
don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.