📖 Zabura 29
-
1
Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
-
2
Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
-
3
Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.
-
4
Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.
-
5
Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
-
6
Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.
-
7
Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.
-
8
Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.
-
9
Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
-
10
Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
-
11
Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.