📖 Zabura 26
-
1
Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.
-
2
Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;
-
3
gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
-
4
Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;
-
5
na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
-
6
Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
-
7
ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
-
8
Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.
-
9
Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai
-
10
waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
-
11
Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
-
12
Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.