📖 Zabura 25
-
1
A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.
-
2
A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
-
3
Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.
-
4
Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka;
-
5
ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.
-
6
Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.
-
7
Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji.
-
8
Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.
-
9
Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
-
10
Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.
-
11
Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.
-
12
To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
-
13
Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
-
14
Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.
-
15
Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
-
16
Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala.
-
17
Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata.
-
18
Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina.
-
19
Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru da kuma yadda suka ƙara ƙina!
-
20
Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka.
-
21
Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka.
-
22
Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu!