📖 Zabura 24
-
1
Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
-
2
gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.
-
3
Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
-
4
Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
-
5
Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
-
6
Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela
-
7
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
-
8
Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.
-
9
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
-
10
Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela