📖 Zabura 21
-
1
Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
-
2
Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
-
3
Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
-
4
Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin
-
5
Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
-
6
Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
-
7
Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.
-
8
Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
-
9
A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
-
10
Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam.
-
11
Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;
-
12
gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.
-
13
Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka.