📖 Zabura 20
-
1
Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
-
2
Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
-
3
Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela
-
4
Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
-
5
Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
-
6
Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.
-
7
Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
-
8
Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.
-
9
Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!