📖 Zabura 19
-
1
Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
-
2
Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani.
-
3
Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su.
-
4
Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
-
5
wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
-
6
Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
-
7
Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.
-
8
Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.
-
9
Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
-
10
Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki.
-
11
Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma.
-
12
Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
-
13
Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye.
-
14
Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.