📖 Zabura 150
-
1
Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
-
2
Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.
-
3
Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,
-
4
yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
-
5
yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
-
6
Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.