1Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?
2Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
4wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,
5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.