📖 Zabura 149
-
1
Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.
-
2
Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
-
3
Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
-
4
Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.
-
5
Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.
-
6
Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,
-
7
don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane,
-
8
don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,
-
9
don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.