📖 Zabura 148
-
1
Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.
-
2
Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
-
3
Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
-
4
Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.
-
5
Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.
-
6
Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
-
7
Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
-
8
walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
-
9
ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,
-
10
namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
-
11
sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
-
12
samari da ’yan mata, tsofaffi da yara.
-
13
Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
-
14
Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.