📖 Zabura 147
-
1
Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
-
2
Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
-
3
Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
-
4
Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.
-
5
Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.
-
6
Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.
-
7
Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu.
-
8
Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
-
9
Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
-
10
Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;
-
11
Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
-
12
Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.
-
13
Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
-
14
Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
-
15
Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.
-
16
Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.
-
17
Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?
-
18
Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.
-
19
Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.
-
20
Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.