1Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.
2Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
3Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
4Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.
5Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
7Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
8Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
9Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
10Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
11Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka,
12saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka.
13Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
14Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
15Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
16Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
17Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.
18Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.