1Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa.
2Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.
3Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi, ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?
4Mutum yana kama da numfashi; kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.
5Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.
6Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba; ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu.
7Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi
8waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
9Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,
10ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa.
11Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
12Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.
13Rumbunanmu za su cika da kowane irin tanadi. Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu, ninki dubu goma-goma a filayenmu;
14shanunmu za su ja kaya masu nauyi. Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu.
15Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.