📖 Zabura 143
-
1
Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini.
-
2
Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
-
3
Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni.
-
4
Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai.
-
5
Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
-
6
Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela
-
7
Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
-
8
Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina.
-
9
Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.
-
10
Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
-
11
Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
-
12
A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne.