📖 Zabura 142
-
1
Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
-
2
Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata.
-
3
Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko.
-
4
Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina.
-
5
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.”
-
6
Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai.
-
7
Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.