📖 Zabura 140
-
1
Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici,
-
2
masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum.
-
3
Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela
-
4
Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
-
5
Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela
-
6
Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.
-
7
Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.
-
8
Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. Sela
-
9
Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.
-
10
Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.
-
11
Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici.
-
12
Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.
-
13
Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.