📖 Zabura 139
-
1
Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.
-
2
Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.
-
3
Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.
-
4
Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
-
5
Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.
-
6
Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.
-
7
Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
-
8
In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can.
-
9
In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku,
-
10
can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.
-
11
In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”
-
12
duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.
-
13
Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
-
14
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.
-
15
Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
-
16
Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.
-
17
Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!
-
18
A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.
-
19
Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!
-
20
Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.
-
21
Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?
-
22
Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana.
-
23
Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata.
-
24
Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya.