1A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.
2A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu,
3gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa?
5In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
6Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba.
7Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!”
8Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana,
9shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.