📖 Zabura 136
-
1
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
2
Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
3
Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
4
Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
5
Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
6
Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
7
Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
8
Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
9
Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
10
Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
11
Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
12
Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
13
Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
14
Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
15
Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
16
Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
17
Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
18
Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
19
Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
20
Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
21
Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
22
Gādo ga bawansa Isra’ila; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
23
Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
24
Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
25
Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
26
Ku yi godiya ga Allah na sama. Ƙaunarsa madawwamiya ce.