📖 Zabura 135
-
1
Yabi Ubangiji. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji,
-
2
ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu.
-
3
Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
-
4
Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
-
5
Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.
-
6
Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
-
7
Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
-
8
Ya kashe ’ya’yan fari na Masar, ’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.
-
9
Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.
-
10
Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna,
-
11
Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana,
-
12
ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila.
-
13
Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.
-
14
Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa.
-
15
Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi.
-
16
Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
-
17
suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu.
-
18
Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.
-
19
Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji; Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;
-
20
Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
-
21
Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji.