📖 Zabura 132
-
1
Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
-
2
Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
-
3
“Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,
-
4
ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,
-
5
sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
-
6
Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,,
-
7
“Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
-
8
ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
-
9
Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
-
10
Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.
-
11
Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,
-
12
in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”
-
13
Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,
-
14
“Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
-
15
zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.
-
16
Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
-
17
“A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
-
18
Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”