📖 Zabura 131
-
1
Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
-
2
Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
-
3
Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.