📖 Zabura 130
-
1
Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
-
2
Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.
-
3
In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
-
4
Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.
-
5
Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
-
6
Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
-
7
Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
-
8
Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.