📖 Zabura 13
-
1
Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?
-
2
Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?
-
3
Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;
-
4
abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.
-
5
Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
-
6
Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri.