📖 Zabura 129
-
1
Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,
-
2
sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.
-
3
Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.
-
4
Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.
-
5
Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.
-
6
Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;
-
7
da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
-
8
Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”