📖 Zabura 128
-
1
Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
-
2
Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.
-
3
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
-
4
Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.
-
5
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
-
6
bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.