📖 Zabura 126
-
1
Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.
-
2
Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “ Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
-
3
Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.
-
4
Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.
-
5
Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
-
6
Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.