📖 Zabura 124
-
1
Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,
-
2
da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,
-
3
sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;
-
4
da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.
-
5
Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.
-
6
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
-
7
Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.
-
8
Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.