1Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
2Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.
3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.
4Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.