📖 Zabura 122
-
1
Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”
-
2
Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.
-
3
An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.
-
4
A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.
-
5
A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.
-
6
Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.
-
7
Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”
-
8
Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”
-
9
Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.