📖 Zabura 121
-
1
Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?
-
2
Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.
-
3
Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
-
4
tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.
-
5
Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
-
6
rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.
-
7
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;
-
8
Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.