📖 Zabura 120
-
1
Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.
-
2
Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.
-
3
Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?
-
4
Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
-
5
Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!
-
6
Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.
-
7
Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.