📖 Zabura 12
-
1
Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
-
2
Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.
-
3
Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,
-
4
masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”
-
5
“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
-
6
Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.
-
7
Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
-
8
Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.