📖 Zabura 119
-
1
Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
-
2
Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
-
3
Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.
-
4
Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.
-
5
Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
-
6
Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
-
7
Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
-
8
Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum. ב Bet
-
9
Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
-
10
Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
-
11
Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.
-
12
Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.
-
13
Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka.
-
14
Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.
-
15
Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.
-
16
Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. ג Gimel
-
17
Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka.
-
18
Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka.
-
19
Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka.
-
20
Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe.
-
21
Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka.
-
22
Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka.
-
23
Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.
-
24
Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. ד Dalet
-
25
An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
-
26
Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka.
-
27
Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.
-
28
Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
-
29
Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.
-
30
Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.
-
31
Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.
-
32
Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata. ה He
-
33
Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
-
34
Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
-
35
Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.
-
36
Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.
-
37
Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
-
38
Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.
-
39
Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.
-
40
Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka. ו Waw
-
41
Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;
-
42
sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.
-
43
Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.
-
44
Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.
-
45
Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.
-
46
Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,
-
47
gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.
-
48
Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka. ז Zayin
-
49
Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege.
-
50
Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.
-
51
Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba.
-
52
Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.
-
53
Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.
-
54
Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka.
-
55
Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.
-
56
Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka. ח Het
-
57
Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka.
-
58
Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.
-
59
Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
-
60
Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.
-
61
Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba.
-
62
Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.
-
63
Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka.
-
64
Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. ט Tet
-
65
Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.
-
66
Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.
-
67
Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.
-
68
Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.
-
69
Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.
-
70
Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.
-
71
Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.
-
72
Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. י Yod
-
73
Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
-
74
Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.
-
75
Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.
-
76
Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.
-
77
Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.
-
78
Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.
-
79
Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.
-
80
Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya. כ Kaf
-
81
Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.
-
82
Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”
-
83
Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.
-
84
Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
-
85
Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.
-
86
Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.
-
87
Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.
-
88
Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka. ל Lamed
-
89
Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.
-
90
Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.
-
91
Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.
-
92
Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana.
-
93
Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
-
94
Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.
-
95
Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.
-
96
Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka. מ Mem
-
97
Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.
-
98
Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.
-
99
Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.
-
100
Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.
-
101
Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.
-
102
Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.
-
103
Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!
-
104
Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba. נ Nun
-
105
Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.
-
106
Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.
-
107
Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
-
108
Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.
-
109
Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba.
-
110
Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.
-
111
Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata.
-
112
Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe. ס Samek
-
113
Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.
-
114
Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.
-
115
Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!
-
116
Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.
-
117
Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
-
118
Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.
-
119
Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka.
-
120
Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka. ע Ayin
-
121
Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni.
-
122
Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni.
-
123
Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci.
-
124
Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
-
125
Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka.
-
126
Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka.
-
127
Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,
-
128
saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba. פ Fe
-
129
Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su.
-
130
Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi.
-
131
Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka.
-
132
Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka.
-
133
Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni.
-
134
Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka.
-
135
Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
-
136
Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. צ Tsade
-
137
Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne.
-
138
Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai.
-
139
Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.
-
140
An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu.
-
141
Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka.
-
142
Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce.
-
143
Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina.
-
144
Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu. ק Kof
-
145
Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.
-
146
Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka.
-
147
Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka.
-
148
Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.
-
149
Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.
-
150
Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka.
-
151
Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne.
-
152
Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada. ר Resh
-
153
Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba.
-
154
Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!
-
155
Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.
-
156
Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.
-
157
Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba.
-
158
Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.
-
159
Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.
-
160
Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne. ש Sin da Shin
-
161
Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.
-
162
Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.
-
163
Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.
-
164
Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci.
-
165
Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.
-
166
Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka.
-
167
Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai.
-
168
Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. ת Taw
-
169
Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.
-
170
Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka.
-
171
Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka.
-
172
Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne.
-
173
Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka.
-
174
Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina.
-
175
Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.
-
176
Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba.