📖 Zabura 118
-
1
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
2
Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
-
3
Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
-
4
Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
-
5
Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.
-
6
Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?
-
7
Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana.
-
8
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.
-
9
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.
-
10
Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
-
11
Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
-
12
Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
-
13
An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni.
-
14
Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.
-
15
Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!
-
16
An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”
-
17
Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
-
18
Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
-
19
Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.
-
20
Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga.
-
21
Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona.
-
22
Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani;
-
23
Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
-
24
Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
-
25
Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
-
26
Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
-
27
Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.
-
28
Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
-
29
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.