📖 Zabura 116
-
1
Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.
-
2
Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.
-
3
Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai.
-
4
Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”
-
5
Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.
-
6
Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.
-
7
Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.
-
8
Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,
-
9
don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
-
10
Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”
-
11
Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”
-
12
Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?
-
13
Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.
-
14
Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.
-
15
Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
-
16
Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.
-
17
Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
-
18
Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,
-
19
a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.