📖 Zabura 115
-
1
Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.
-
2
Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?”
-
3
Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama.
-
4
Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.
-
5
Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
-
6
suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi
-
7
suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.
-
8
Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.
-
9
Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
-
10
Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
-
11
Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
-
12
Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna,
-
13
zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka.
-
14
Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku.
-
15
Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa.
-
16
Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum.
-
17
Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji, waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru;
-
18
mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.