📖 Zabura 114
-
1
Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,
-
2
Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.
-
3
Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;
-
4
duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.
-
5
Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,
-
6
ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?
-
7
Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,
-
8
wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.