📖 Zabura 11
-
1
A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.
-
2
Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu; sun kuma ɗana kibiyoyinsu don su harbi mutanen kirki a zuciya daga cikin duhu.
-
3
Sa’ad da aka tumɓuke tushe, me adali zai iya yi?”
-
4
Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.
-
5
Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.
-
6
A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu.
-
7
Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.