📖 Zabura 108
-
1
Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
-
2
Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.
-
3
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.
-
4
Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.
-
5
A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
-
6
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
-
7
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
-
8
Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta.
-
9
Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”
-
10
Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?
-
11
Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
-
12
Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.
-
13
Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.