📖 Zabura 107
-
1
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
2
Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
-
3
su da ya tattara daga ƙasashe, daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
-
4
Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada, ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba.
-
5
Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya.
-
6
Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu.
-
7
Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna.
-
8
Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
-
9
gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
-
10
Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,
-
11
gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.
-
12
Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.
-
13
Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.
-
14
Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu.
-
15
Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
-
16
gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.
-
17
Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.
-
18
Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.
-
19
Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.
-
20
Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.
-
21
Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
-
22
Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.
-
23
Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.
-
24
Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.
-
25
Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.
-
26
Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.
-
27
Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.
-
28
Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.
-
29
Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.
-
30
Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.
-
31
Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
-
32
Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa.
-
33
Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,
-
34
ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.
-
35
Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;
-
36
a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.
-
37
Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona;
-
38
ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.
-
39
Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;
-
40
shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.
-
41
Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.
-
42
Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.
-
43
Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.