📖 Zabura 106
-
1
Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
-
2
Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa?
-
3
Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.
-
4
Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
-
5
don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.
-
6
Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
-
7
Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
-
8
Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.
-
9
Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.
-
10
Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.
-
11
Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.
-
12
Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.
-
13
Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.
-
14
A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
-
15
Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.
-
16
A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.
-
17
Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.
-
18
Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye.
-
19
A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.
-
20
Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.
-
21
Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,
-
22
mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.
-
23
Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.
-
24
Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.
-
25
Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.
-
26
Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,
-
27
ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.
-
28
Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;
-
29
suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.
-
30
Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina.
-
31
An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa.
-
32
A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su;
-
33
saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.
-
34
Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba,
-
35
amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu.
-
36
Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.
-
37
Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu.
-
38
Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
-
39
Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
-
40
Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.
-
41
Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.
-
42
Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.
-
43
Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.
-
44
Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;
-
45
saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.
-
46
Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.
-
47
Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.
-
48
Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji.