📖 Zabura 105
-
1
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
-
2
Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
-
3
Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
-
4
Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
-
5
Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi, mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
-
6
Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.
-
7
Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.
-
8
Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
-
9
alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.
-
10
Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,
-
11
“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.”
-
12
Sa’ad da suke kima kawai, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
-
13
suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga masarauta zuwa wata.
-
14
Bai bar kowa yă danne su ba; saboda su, ya tsawata wa sarakuna,
-
15
“Kada ku taɓa shafaffena; kada ku yi wa annabawa lahani.”
-
16
Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;
-
17
ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.
-
18
Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa,
-
19
sai abin da ya rigafaɗi ya cika sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya.
-
20
Sarki ya aika aka kuma sake shi, mai mulkin mutane ya ’yantar da shi.
-
21
Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka,
-
22
don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama yă kuma koya wa dattawa hikima.
-
23
Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.
-
24
Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa; ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu,
-
25
waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa.
-
26
Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.
-
27
Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.
-
28
Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu, ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba?
-
29
Ya mai da ruwaye suka zama jini, ya sa kifayensu suka mutu.
-
30
Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi, waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.
-
31
Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.
-
32
Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da walƙiya ko’ina a ƙasarsu;
-
33
ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu ya ragargaza itatuwan ƙasarsu.
-
34
Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito, fāran da ba su ƙidayuwa;
-
35
suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu, suka cinye amfanin gonarsu
-
36
Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu, nunan fari na dukan mazantakarsu.
-
37
Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.
-
38
Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.
-
39
Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare.
-
40
Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.
-
41
Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.
-
42
Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.
-
43
Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;
-
44
ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,
-
45
don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.