📖 Zabura 104
-
1
Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.
-
2
Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti
-
3
ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska.
-
4
Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.
-
5
Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.
-
6
Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.
-
7
Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;
-
8
suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.
-
9
Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.
-
10
Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu.
-
11
Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.
-
12
Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa.
-
13
Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.
-
14
Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,
-
15
ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.
-
16
Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka.
-
17
A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.
-
18
Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.
-
19
Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.
-
20
Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.
-
21
Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah.
-
22
Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu.
-
23
Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma.
-
24
Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.
-
25
Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.
-
26
A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.
-
27
Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.
-
28
Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.
-
29
Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura.
-
30
Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya.
-
31
Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,
-
32
shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.
-
33
Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
-
34
Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
-
35
Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.